22 Janairu 2026 - 20:24
Source: ABNA24
Hashdush Sha'abi Su Na Cikin Shirin Kota Kwana

Hashdush Shaabi su na cikin shirin ko-ta-kwana wajen fuskantar ƴan ta'addan Da'ish

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Faleh Fayyadh, shugaban kungiyar Hashdush Sha'abi na Iraki, ya ba da umarni ga dukkan sassan da mukamai na wannan ƙungiya, ƙaruwar taka tsantsan da ƙarin tsaro da cikakken shiri kan yiwuwar barazanar da duk wani yunkuri na "kutsawa, duk wani yunƙurin da ake shakku akai ko barazanar ta'addanci" akan yankin Iraki.

Hakan ya biyo bayan hatsarin dake fuskantar Iraki da Siriya bayan da ƴan ta'addan Nusra bayan sako ƴan ta'addan ISIS sun ce musu: Duk inda kuke son zuwa kuje, kada ku bar wannan damar ta kubece ma ku.

Bayan rugujewar dakarun QASD daga sansanin Al-hul, inda ake tsare da dubban iyalan ISIS, dakarun kungiyar Al-Julani na Jabhatun-Nusra sun 'yantar da wani adadi mai yawa na kawayensu wajen kisan da laifukann ta'addanci a Siriya da suka shafe fiye shekaru goma suna aikatawa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha